ABNA24 : Tashe tashen hankula sun tilastawa mutane sama da dubu 537 tserewa daga gidajensu, kamar yadda ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD OCHA ya bayyana.
Kana matsalar ta shafi rayuwar mutane wajen hana su samun damar amfani da muhimman kayayyakin more rayuwa, kamar ilimi da kiwon lafiya.
Mayaka masu ikirarin kishin addini, daga yankunan kudancin Sahel, su ne suka addabi mazauna yankin.
A cewar ofishin, kimanin mutane miliyan 3.8 a jamhuriyar Nijar ne ke bukatar tallafin jinkai a wannan shekarar.
Hukumomin bayar da agajin suna bukatar kudi dala miliyan 523 don tallafawa mutane sama da miliyan 2, sai dai kashi 8 bisa 100 na kudaden da ake bukatar ne kawai aka samu a halin yanzu.
342/